Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar tsaron Najeriya ta karyata rahotannin amfani da wasu kaburburan sirri a yankin arewa maso gabashin kasar
2019-08-02 09:19:32        cri
Hedkwatar tsaron Najeriya, ta karyata wasu rahotanni dake wadari cewa, wai sojoji na amfani da wasu kaburburan sirri a yankin arewa maso gabashin kasar, inda suke binne gawarwakin wasu daga dakarunta a asirce.

Mai magana da yawun hedkwatar tsaron Najeriyar Onyema Nwachukwu, ya bayyana cikin wata sanarwar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafenta a Legas cewa, wannan zargi ko kadan babu kamshin gaskiya a cikinsa, kuma hakan ya saba al'ada da tsarin aikin soja.

Ya ce, makabartan da ake magana cikin rahotan, wanda ke barakin soja na Maimalari, makabartan sojojin badujala dake yankin arewa maso gabashin Najeriya a hukumance, an kuma gina wata runfa a kusa da wurin don karrama dakarun da suka kwanta dama a fagen daga.

Don haka, hedkwatar tsaron ta bukaci dakarunta da ma daukacin jama'a, da su yi watsi da irin wadannan rahotanni marasa tushe kana shaci fadi ne na marubucin, wanda ba shi da masaniya game da ka'ida da tsarin aikin soja.

Wasu rahotannin dake yawo a kafofin sada zumunta ne, suke zargin sojoji da amfani da wasu kaburbura na sirri a yankin arewa maso gabashin kasar, wajen binne gawawwakin sojojin da aka dauko a boye daga dakin ajiye gawawwaki. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China