Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An zabi Ramaphosa a matsayin shugaban Afirka ta kudu
2019-05-23 10:12:49        cri

A jiya ne 'yan majalisar dokokin kasar Afirka ta kudu, suka zabi Cyril Ramaphosa a matsayin shugaban jamhuriyar Afirka ta kudu.

Da yake jawabi bayan zaben nasa, Ramaphosa, ya ce, ya ji dadin yadda aka karrama shi, bisa sake zabarsa domin ya bautawa jama'ar Afirka ta kudu. Yana mai cewa, zai zama shugaban daukacin 'yan kasar, kana a matsayinsa na shugaba, ya yi alkawarin gudanar da ayyuka masu kyau ga kasa, biyo bayan zabensa da talakawan kasar suka yi.

Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, wajibi ne Ramaphosa ya kama aiki cikin kwanaki biyar bayan shan rantsuwa ko tabbatar da biyayyarsa ga jamhuriya da mutunta kundin tsarin mulkin kasar.

A ranar 25 ga watan Mayu ne, ake saran Ramaphosa zai yi rantsuwar kama aiki, yayin bikin rantsar da shi, da za a shirya a birnin Pretoria.

Jam'iyyarsa ta ANC ce dai ta tsayar da shi takara, inda ya samu kaso 57.51 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben shugabancin kasar na ranar 8 ga watan Mayun wannan shekara, sai dai a wannan karo,kujerun da jam'iyyar ta saba samu a zabukan majalisar dokokin kasar sun ragu.

Nasarar da jam'iyyar ANC ta samu a zabukan kasar, ita ce ta baiwa Ramaphosa damar samun wa'adin shugabancin kasar. Amma duk da haka, sai 'yan majalisar dokokin kasar dake cikin sabuwar majalisar sun kada kuri'ar amincewa, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China