Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cutar kyanda ta hallaka mutane 100 a arewa maso gabashin Najeriya
2019-08-01 10:52:26        cri
Hukumomin lafiya sun tabbatar da cewa kimanin mutane 100 ne suka mutu a sanadiyyar cutar kyanda a jahohi biyu a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya a cikin wannan shekarar.

Jami'an kiwon lafiya na jahohin Borno da Yobe sun ce an samu adadin wadanda suka kamu da cutar kyanda 20,879, a jahohin biyu tun daga watan Janairu.

Sule Mele, shugaban hukumar lafiyar matakin farko na jahar Borno, ya ce, an samu adadin bullar cutar kyandar 18,204 a jahar, sannan an samu hasarar rayuka 93, galibinsu kananan yara ne, tun daga farkon wannan shekarar.

Mele ya danganta yaduwar cutar sakamakon rashin samun damammakin kayayyakin kiwon lafiya a sansanonin 'yan gudun hijira, saboda rashin tsaro, da yaki tsakanin jami'an tsaro da mayakan Boko Haram.

Jami'in lafiyar ya ce, hukumar lafiya matakin farko tana ci gaba da sanya ido, da bin diddigin barkewar cutar, da kuma gudanar da gwaje-gwaje, da rigakafi a yankunan da cutar ta shafa. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China