Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin sunayen ministocin da aka gabatar mata
2019-07-31 10:18:07        cri
Majalisar dattawan Najeriya, ta tabbatar da nadin dukkan sunayen ministocin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya gabatar mata.

Shugaban majalisar dattawan kasar, Ahmed Lawan, shi ne ya tabbatar da hakan, bayan da dafatalin ministocin suka bayyana amincewarsu a karshen shirin tantance ministoci 43 din da majalisar ta shafe kwanaki biyar tana yi,

A ranar Talatar da ta gabata ce, shugaba Buhari ya aikawa majalisar dattawan sunayen da yake son nadawa a matsayin ministocinsa, bayan jinkirin watanni biyu na nada ministocin, tun bayan da shugaban ya sha rantsuwar kama aiki a wa'adin mulkinsa na biyu a ranar 29 ga watan Mayu.

Kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada, sai majalisar dattawan kasar ta tantace ministocin kafin su fara aiki, a ranar Larabar da ta gabata ce dai, majalisar dattawan ta fara tantance ministocin. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China