Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci kasashen Afrika su hada kai don tunkarar kalubalolin dake damun nahiyar
2019-08-07 11:07:09        cri
Shugaban majalisar kasashen Afrika Roger Nkodo Dang, ya bukaci kasashen Afrika su hada kai don yin aiki tare da nufin kyautata makomar nahiyar domin amfanawa al'ummar kasashen.

Dang ya bayyana hakan ne a Johannesburg, a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron shugabannin majalisar ministocin kasashen Afrika.

Ya bukaci shugabannin majalisun da su tunkari kalubalolin dake damun kasashen Afrika, kuma su yi kyakkyawan amfani da duk wasu damammakin da ake da su.

Ya ce, wajibi ne a samu hadin kai tsakanin al'ummar kasashen Afrika domin samun dawwamamman zaman lafiya, wanda shi ne ginshikin da zai tabbatar da dorewar demokaradiyya.

Shugabar kungiyar gamayyar majalisun kasashen duniya, Gabriela Cuevas Barron, ta bukaci kasashen Afrika su yi aiki tare wajen yakar tsattsauran ra'ayi, da ta'addanci, da sauyin yanayi, da samarwa matasa ayyukan yi. Ta kara da cewa, yarjejeniyar AfCFTA zata bunkasa tattalin arzikin mafi yawan kasashen Afrika idan aka aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.

Shugabannin majalisu daga kasashen Afrika da dama suna gudanar da taron tattaunawa domin nazarin manyan kalubalolin dake addabar nahiyar. An bude taron ne a ranar Litinin wanda ake sa ran kammalawa a ranar Asabar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China