Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani kamfanin kasar Sin ya dauki nauyin shimfida layin dogon da ya hada Angola da Tanzania
2019-08-05 15:22:15        cri
A kwanan baya, wani jirgin kasa mai dauke da masu yawon shakatawa ya tashi daga Lobito dake bakin tekun kasar Angola, zuwa Dar es Salaam dake bakin tekun kasar Tanzania, kan layin dogo na Benguela. Hakan ya kasance karon farko da wani jirgin kasa ya tashi daga bakin tekun yammacin Afirka, ya kama hanyar zuwa bakin teku dake gabashin nahiyar.

Wani kamfani na kasar Sin mai taken "China Railway Twentieth Bureau Group Co." ne ya dauki nauyin shimfida wannan layin dogo da ya ketare kasar Angola. Ya kuma hada wannan layi da layin dogon da ya hada Tanzania da Zambia, da kasar Sin ta ba da tallafi wajen gina shi a shekarun 1970. Ta wannan hanya, za a taimakawa musayar tsakanin kasahsen Tanzania, Zambia, DRC, da kuma Angola, haka kuma za a kara azama ga yunkurin raya tattalin arziki, da yawon bude ido a wasu yankunan dake bakin tekun kasashen Angola, da Tanzania. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China