Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rashawa da rashin managarcin jagoranci ne manyan matsalolin Afirka in ji wani minista
2019-08-07 10:56:38        cri
Ministan ma'aikatar kula da harkokin fadar shugaban kasa, da ayyukan hukuma a kasar Botswana Nonofo Molefhi, ya yi kira ga masu shiga tsakani, da masu tallafawa ayyukan sulhu a nahiyar Afirka, da su yi yaki da cin hanci da rashawa, da jagoranci maras inganci, kasancewar su manyan matsaloli dake dakile ci gaban nahiyar.

Mr. Molefhi ya bayyana hakan ne a jiya Talata a birnin Gaborone, yayin taron kungiyar masu shiga tsakani da ayyukan sulhu ta kasashen kudancin Afirka ko AOMA a takaice, yana mai cewa wadannan matsaloli guda biyu, na zama alakakai ga tattalin arziki, da shugabancin ko wace irin kasa.

Molefhe ya kara da cewa, rashawa da rashin shugabanci na gari, na karya managarcin tsarin kiwon lafiya, da wadata, da kuma makomar kasashe. Jami'in ya nuna damuwa da cewa, duk da irin dunbin albarkatu da Afirka ke da su sama da wasu yankuna, nahiyar na fuskantar tarin matsalolin ci gaba, sakamakon wadannan matsaloli biyu.

Taron na AOMA dai ya hada wakilai daga kasashen Angola, da Botswana, da Lesotho, da Malawi, da Mozambique. Sauran su ne Namibia, da Afirka ta kudu, da Zambia da kuma Zimbabwe. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China