Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai bukatar kasashen Afirka su sanya hannu kan yarjejniyar hukumar harhada magunguna ta Afirka
2019-08-05 09:53:07        cri
Masana da masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya daga Afirka, sun yi kira ga mahukuntan kasashen nahiyar, da su rattaba hannu kan yarjejniyar hukumar harhada magunguna ta Afirka ko AMA a takaice.

Masanan sun bayyana hakan ne yayin taron ministoci na kasashen nahiyar da ya gudana a karshen mako, domin tattauna batutuwa da suka shafi kiwon lafiya, da yawan al'umma, da kuma kula da magunguna.

Taron wanda ya gudana karkashin lemar kwamitin musamman na kungiyar AU, ya ja hankalin masu ruwa da tsaki daga nahiyar da su rungumi wannan yarjejeniya, ko a kai ga hade tsarin kula da harhada magungun na Afirka wuri guda, ta yadda hakan zai kawo babban sauyi a fannin harhada magunguna a nahiyar Afirka baki daya.

Da take tsokaci game da batun, kwamishiniyar AU mai kula da harkokin al'umma Amira Elfadil, ta ce AU za ta hanzarta wajen amincewa da yarjejeniyar ta AMA. Elfadil ta kuma bayyana aniyar kungiyar, ta yayata bukatar samar da kudade a cikin gida, da hadin gwiwa a fannin ayyukan kiwon lafiya, da daidaita tsare tsaren bada tallafi daidai da bukatun al'ummar kasashen nahiyar, kamar yadda hakan yake kunshe cikin ajandar raya Afirka nan da shekarar 2063. Elfadil, ta kuma jinjinawa kwazon kasashe 4 mambobin kungiyar AU, da tuni suka sanya hannu kan takardun wannan yarjejeniya ta AMA. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China