Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci kasashen Afrika su yi amfani da yarjejeniyar AfCFTA don bunkasa cinikin Afrika
2019-08-03 15:28:56        cri
Hukumar kula da tattalin arzikin kasashen Afrika ta MDD (ECA), ta bukaci kasashen shiyyar Afrika da su yi amfani da damar yarjejeniyar ciniki maras shinge (AfCFTA), domin bunkasa matsayin cinikayya a tsakanin kasashen Afrika.

Hukumar ECA, ta lura cewa, Afrika ita ce nahiyar dake sahun baya wajen aiwatar da cinikayya tsakanin kasashen shiyyar idan an kwatanta da sauran nahiyoyin duniya, inda ta jaddada irin gagarumin muhimmancin da yarjejeniyar AfCFTA ke da shi wajen kawo sauye sauye game da dangantakar ciniki tsakanin kasashen Afrika har ma da sauran kungiyoyin cinikayya na shiyyar baki daya.

A cewar ECA, ana sa ran yarjejeniyar AfCFTA za ka bunkasa cinikayya tsakanin kasashen Afrika da sama da kashi 50 bisa 100, yayin da ma'aunin GDP na shiyyar zai karu da sama da dala biliyan 40, kana za ta fitar da hajoji zuwa ketare na sama da dala biliyan 55.

Sai dai hukumar MDDr, ta jaddada cewa yarjejeniyar AfCFTA za ta samu nasarar cimma burin bunkasa cinikayya tsakanin kasashen nahiyar ne idan har kasashen shiyyar sun bayar da cikakken goyon bayansu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China