Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci kasashen Afrika su mayar da hankali kan yadda za su biya bashi maimakon yawan bashin da ake binsu
2019-08-02 10:55:39        cri

Hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA), ta jaddada bukatar kasashen Afrika su rika mayar da hankali kan karfin iya biyan bashin da suka karba daga ketare, maimakon yawan bashin da ake binsu.

Sakatariyar zartarwa ta hukumar Vera Songwe ce ta bayyana haka ga Gwamnonin manyan bankunan kasashen, inda ta ce, kula da yadda za a biya bashi ya dogara ne kan daukar kyawawan manufofin rage kudin da gwamnati ke kashewa, wadanda ke da alaka da ingantacciyar manufar sanya ido kan harkokin kudi.

Ta kuma jaddada cewa, yanayin da ake ciki yanzu, na samu saukin karbar bashi, saboda karancin kudin ruwa daga kasashen masu karfin tattalin arziki, bai samar da wani ci gaba ga kasashen nahiyar ba.

Hukumar ECA ta yi kiyasin Afrika na bukatar dala biliyan 638 a kowacce shekara domin cimma burinta na samun ci gaba, yayin da kudin da ake bukata na cimma muradun ci gaba masu dorewa ya zuwa shekarar 2030, a tsakanin kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga ya kai dala triliyan 1.2 a kowacce shekara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China