Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamata ya yi kasashen Afirka su waiwayi kasuwar yawon shakatawa ta kasar Sin
2019-07-26 10:36:26        cri

Tsoho babban sakataren hukumar MDD mai lura da harkokin yawon bude ido Taleb Rifai, ya ce ya kamata kasashen dake nahiyar Afirka, su mai da hankali ga kasuwar yawon shakatawa ta kasar Sin.

Mr. Rifai, ya ce akwai bukatar mahukuntan kasashen nahiyar su mai da hankali, ga magance matsalolin dake kawo nakasu ga harkokin yawon shakatawa, wadanda ke hana masu sha'awa zuwa kasashen nahiyar.

Tsohon jami'in ya yi wannan tsokaci ne, yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Alhamis, biyowa bayan wani taron masu ruwa da tsaki.

Ya ce yawon shakatawa sabon arziki ne ga kasashen nahiyar wanda ribarsa ba ta yankewa, yana kuma samar da guraben ayyukan yi masu tarin yawa. Kaza lika gwargwadon kulawar da aka nunawa sashen, gwargwadon irin ribar da za a girba daga gare shi. Rifai ya kuma ce kasar Sin na cikin kasashe na kan gaba a fannin yawan masu fita yawon bude ido, wadanda a kullum yawansu ke karuwa.

A masa tsokacin kuwa, tsohon ministan ma'aikatar yawon bude ido da raya al'adu na kasar Seychelles Alain St. Ange, cewa ya yi ya dace kasashen Afirka su lura da kasuwar Sin a fannin yawon bude ido, duba da yawan al'ummarta. Har ila yau kamata ya yi a samar da masu jin harshen Sinanci a wasu muhimman wuraren yawon bude ido, domin saukaka wa Sinawa masu ziyarar wadannan wurare.

A nasa bangare kuwa, babban sakatare a ma'aikatar muhalli, yawon bude ido da nishadantarwa na kasar Zimbabwe Munesushe Munodawafa, cewa ya yi a halin yanzu, yawan Sinawa mawadata na karuwa, wanda hakan ke samar da karin yawan masu sha'awar zuwa yawon bude ido. Don haka baya ga ofishi da kasarsa ta bude a birnin Beijing, a yanzu haka suna shirin bude wani ofishi a birnin Shanghai, da ma karin wasu biranen Sin guda biyu, domin tallafawa masu sha'awar zuwa Zimabwe yawon shakatawa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China