![]() |
|
2019-08-02 11:17:26 cri |
Babban direktan jaridar Vanguard Soni Daniel ya wallafa wani rahoto mai taken "Sin: Kasa mai yawan mutane dake da hanyoyi da dama na samun bunkasuwa" a ran 27 ga watan Yuli. Sannan wani dan kasuwar Nijeriya mai suna Sunny Ikhioya, shi ma ya rubuta wani sharhi a jaridar Vanguard da aka wallafa a ran 31 ga watan Yuli mai taken "Sin tana ci gaba yadda ya kamata, wace hanya Nijeriya ta dosa?", wadannan sharhohi biyu sun bayyana abin da suka gani yayin ziyararsu a kasar Sin.
A cikin sharhinsa, Soni Daniel ya nuna cewa, bai taba ziyartar birnin Beijing ba, an gayyace shi wani kwas din samun horas da aka gabatarwa kafofin yada labarai na kasashe dake cikin shawawari "Ziri daya da hanya daya", a waccan lokaci, ya ganewa idonsa halin da birnin Beijing ke ciki a matsayinta cibiyar kasuwanci ta nahiyar Asiya.
A cikin sharhin, Sunny Ikhioya ya bayyana cewa, babu bambancin launin fata da rikicin addini a kasar Sin ko kadan, kowa na yi kokarin ba da gudunmawarsa wajen raya kasar. Sin ta samu nasarori a yau ne ta hanyar yin kokari matuka. Ya kamata Nijeriya ta koyi fasahar kasar Sin tare da kara zage damtse ta yadda za ta yi nasarar sauya al'amura da ciyar da kasa gaba. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China