Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta daui matakan sa kaimi ga kiwon lafiyar tsofaffi
2019-07-30 15:10:12        cri
Sin kasa ce dake kan gaba wajen yawan tsofaffi a duniya, kana tana daya daga cikin kasashe da yawan tsofaffi ke karuwa cikin sauri a duniya. Ya zuwa karshen shekarar 2018, yawan tsofaffi da shekarunsu suka zarce 60 a kasar Sin ya kai miliyan 249, wanda ya kai kashi 17.9 cikin dari na adadin al'ummar kasar. A yayin taron manema labarun da aka gudanar a ranar 29 ga wannan wata, shugaban ofishin kula da lafiyar tsofaffi na hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Wang Haidong ya bayyana cewa, ana fuskantar matsala game da lafiyar tsofaffi a kasar.

A kwanakin baya, Sin ta gabatar da shirin kiwon lafiya na shekarar 2019 zuwa 2030, game da wannan batu, Wang Haidong ya yi bayani cewa, ya kamata a dauki matakan inganta kiwon lafiyar tsofaffi. A tabbatar da ingancin abincinsu, da motsa jiki, da yin binciken lafiyarsu, da lafiyar jiki da kuma a zuciya, da yadda za su rika shan magani da sauransu, da kyautata tsarin bada hidimar kiwon lafiyar tsofaffi da manufofin kiwon lafiyar tsofaffi a unguwoyi, da kokarin hade tsarin bada jinya da kiwon lafiya, da neman cimma tsarin inshorar kulawa, da samar da yanayin wurin zauna na tsofaffi da suka dace, matakan da za su taimaka ga lafiyar tsofaffi yadda ya kamata. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China