Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin gine gine gidajen kwana na Sin za su samar da turakun cajin ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi
2019-07-29 20:40:59        cri
Wasu manyan kamfanonin gine gine gidajen kwana dake kasar Sin guda hudu, sun sha alwashin samar da turakun cajin ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi, domin amfanin mazauna unguwanni da yawan su zai kai miliyan 8.7.

An ce turakun za su baiwa masu amfani da su damar biyan kudi ta fasahar QR, idan har suna son yiwa ababen hawan su caji.

Sin ce kasa ta daya a yawan ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi a duniya, inda ya zuwa karshen watan Yuni, yawan turakun cajin ababen hawa a sassan kasar suka kai miliyan daya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China