![]() |
|
2019-07-30 11:09:41 cri |
A gun taron tattaunawa mai taken "rawar da kasashe masu tasowa ke taka wajen kare dokokin kasa da kasa sakamakon manyan sauye-sanye da ake fuskanta a duniya" da aka gudanar a wannan rana, jami'an tsara dokoki da na ofisoshin jakadancin kasashe masu tasowa fiye da 80 dake kasar Sin, da wakilan MDD, da kungiyar agaji ta Red Cross da sauran kungiyoyin duniya, da masana fiye da 300 sun tattauna tare.
Shugaban cibiyar nazarin dokokin kasa da kasa ta Afirka Sani Mohamed ya bayyana cewa, Sin ta taba jagorantar kasashen Afirka shiga harkokin duniya, da taimaka musu wajen shiga tsarin odar kasa da kasa. Kasashen Afirka sun nuna godiya ga kasar Sin bisa ga muhimmiyar rawa da ta taka wajen tabbatar da kare dokoki da odar kasa da kasa.
Forfesa James Jassy na jami'ar Loyola ta kasar Amurka ya bayyana cewa, wasu kasashe sun janye daga kungiyoyin kasa da kasa da yarjejeniyoyin duniya, wanda ya kawo kalubale ga ra'ayin kasancewar bangarori daban daban a duniyarmu. Amma kasashe masu tasowa da dama sun yi kokarin shiga aikin tafiyar da harkokin duniya da tabbatar da dokokin kasa da kasa. Ta hanyar yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa ne kadai, za a iya daidaita matsalolin bunkasuwa, da sauyin yanayi, da cinikin duniya da sauransu da dan Adam ke fuskanta. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China