Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Nijeriya ya ce yanzu tafkin Chadi ba mafaka ne ga kungiyar Boko Haram ba
2019-05-17 09:59:02        cri
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya ce yanzu tafkin Chadi ba mafaka ne ga kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram ba, la'akari da yadda kokarin sojojin kawance na kasashen yankin ya haifar da kyakkyawan sakamako.

Muhammadu Buhari, ya bayyana haka ne a jiya, yayin rufe taro na 16 na shekara-shekara na kwamitin shugabannin rudunonin 'yan sandan yammacin Afrika da taron ministocin dake kula da harkar tsaro da ya gudana a Abuja, babban birnin Nijeriya.

Shugaban wanda ya samu wakilcin Ministan harkokin cikin gidan kasar Abdurrahman Dambazau, ya ce sojoji sun gudanar da ayyuka tukuru kan 'yan ta'addan, ta hanyar sake fasalin rundunar kawancen sojin, wadda ta karya lagonsu.

Ya ce a cikin shekaru 4 da suka gabata, Nijeriya da hadin gwiwar kasashen yankin, sun dauki matakai sosai kuma ba su yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da Boko Haram.

Shugaban ya bukaci shugabannin tsaro na kasashen yankin da su yi musayar dabaru, tare da sake nazari ayyukansu da takaita laifukan da ake aikatawa a kasashensu, domin ganin kawar da kungiyar ta'addan.

Muhammadu Buhari ya kuma alakanta raunin da yankin ke da shi da laifukan da ake aikatawa da sauran bazaranar tsaro da zaman lafiya, da manyan iyakokinsu da kuma saukin isa yankin Sahel.

Kasashen da suka halarci taron na Abuja, sun hada da Burkina Faso da Cape Verde da Benin da Cote d'Ivoire da Gambia da Ghana da Guinea da Guinea Bissau da Liberia da Mali da Niger da Senegal da Saliyo da kuma Togo. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China