Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojin Nijeriya ta zargi kungiyoyin agaji da tallafawa kungiyar Boko Haram
2019-05-31 10:21:24        cri

Rundunar sojin Nijeriya, ta zargi kungiyoyin agaji dake aiki a yankin arewa maso gabashin Nijeriya dake fama da rikici, da taimakawa kungiyar Boko Haram, tana mai gargadinsu a kai.

kakakin rundunar, Sagir Musa, wanda ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, ya ki bayyana sunayen kungiyoyin da ake zargi da bada taimako kamar na kayayyakin abinci ga kungiyar Boko Haram.

Sai dai, ya tabbatar da cewa an kama wani kusa cikin mayakan Boko Haram yayin da yake karbar kayayyakin abinci daga wata kungiyar agaji dake aiki a yankin arewa maso gabashin kasar da ake yaki da 'yan ta'adda.

Sagir Musa ya kuma bayyana lamarin a matsayin yi wa tsaron kasar katsalandan, yana mai bukatar kungiyoyin da su kaurace daga yi wa tsaron kasar da yaki da kungiyar 'yan ta'addan tarnaki.

Rundunar sojin ta kara da cewa, ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen kakaba takunkumi kan kungiyar da ki jin gargadin, tana mai kira a gare su da su gudanar da ayyukansu bisa ka'idojin aikin agaji, kuma bisa ka'idoji da dokokin aikin jin kai na kasa da kasa da na rikici. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China