Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mayakan Boko Haram sun halaka mutane 16 a Najeriya
2019-05-27 21:06:11        cri
Mai magana da yawun kungiyar 'yan kato da goro dake taimakawa sojoji a yakin da suke yi da 'yan ta'adda Bello Danbatta, ya bayyana cewa, 'yan ta'addan Boko Haram, sun kashe mutane 16 ciki har da 'yan kungiyar, a wani sabon hari da suka kaddamar a jihar Borno mai fama da tashin hankali dake yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Jami'in ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an kashe 'ya'yan kungiyar ta JTF biyar da wasu kauyawa 11, lokacin da mayakan Boko Haram suka farma wasu kauyuka biyu dake wajen Maiduguri, fadar mulkin jihar Borno a jiya Lahadi.

Ya ce, mutane da dama ne suka jikkata sanadiyar harin. Galibin kauyawan dai sun gudu zuwa cikin daji don tsira da rayukansu, yayin da maharan ke harbin kan mai uwa da wabi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China