Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Koyon harshe na da muhimmanci ga alakar al'adu tsakanin Sin da Afirka
2019-07-23 19:55:15        cri

Masani a cibiyar nazarin harkokin shugabanci ta Thabo Mbeki dake kasar Afirka ta kudu, Farfesa Paul Tembe, ya bayyana cewa, yadda ake samun karuwar jami'o'in Afirka da na Sin dake koyar da dalibansu harsunan juna ba wani sabon abu ba ne.

Bayanan Tembe na zuwa ne bayan da jami'ar koyar da harsunan waje ta Beijing ta kasance jami'a ta baya-bayan nan dake koyar da dalibai dake neman digiri na farko harshen isiZulu. Haka kuma jami'ar ta wallafa kamus din harshen isiZulu da littattafan Sinanci.

Masanan ya ce, za a samu karin jami'o'in kasar Sin da za su koyar da harsunan Afirka, kana za a samu dalibai a nahiyar Afirka da za su karanta harshen Sinanci. Shi dai Farfesa Temba yana da digiri na uku a fannin nazarin harshen Sinanci. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China