2019-07-25 10:32:07 cri |
Mr. Mueller wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin zaman kwamitin shari'a na majalissar dokokin Amurka, ya ce ba zai iya tabbatar da ko shugaban kasar ya aikata laifi ko a'a ba.
A daya bangaren kuma, Mueller ya ce ba zai iya amsa tambaya game da abubuwa da ka iya shafar al'ummar kasar ba, ciki hadda tushen bincike, wanda hukumar bincike ta FBI ta gudanar, game da wancan batu na zargin yunkurin murde zabe da ake wa kasar Rasha. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China