Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump: kamfanonin Amurka su iya ci gaba da samar da kayan aiki ga kamfanin Huawei
2019-06-29 16:58:06        cri
A wurin taron manema labaru da aka gudanar bayan rufe taron koli na kungiyar G20 na birnin Osaka, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, kamfanonin kasarsa su iya ci gaba da samar da kayayyakin aiki ga kamfanin Huawei.

Shugaba Trump ya bayyana cewa, yawan kudin da kamfanonin Amurka suka samu daga sayar da kayayyaki ga kamfanin Huawei a kowace shekara ya kai fiye da dala biliyan 10. Game da batun ko janye kamfanin Huawei daga jerin sunayen kamfanonin da kasar Amurka ta kayyade fitar da kayayyaki gare su, Trump ya ce za a tattauna batun a cikin wasu kwanaki masu zuwa. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China