Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta yiwa kawayenta na Turai barazanar sanya takunkumi kan batun nukiliyar Iran
2019-05-30 11:08:21        cri
Gwamnatin Amurka ta aike da sakon gargadi ga kawayenta na kasashen Turai inda ta ce za su iya fuskantar takunkumi muddin yarjejeniyar tattalin arzikin da suka kulla na kasuwanci da Iran ta fara aiki, kafafen yada labaran Amurkar ne suka bada rahoton a jiya Laraba.

A watan Janairu kasashen Birtaniya, Faransa da Jamus suka bada sanarwar kafa wani tsarin tallafawa mu'amalar cinikayya da ake kira INSTEX, a matsayin wani sabon salon tafiyar da mu'amalar ciniki da kasar Iran da nufin tabbatar da yarjejeniyar nukiliyar Iran din wacce aka kulla.

A wasikar da ya rubutawa shugaban shirin na INSTEX Per Fischer, a ranar 7 ga watan Mayu, babban jami'i mai kula da ayyukan ta'addanci da bayanan sirri na harkokin kudaden Amurka, Sigal Mandelker, ya bayyana shirin na INSTEX, da kuma duk wani mai alaka da shirin, na iya fuskantar takunkumin tattalin arziki daga gwamnatin Amurka idan har shirin ya fara aiki, kamar yadda kafar yada labarai ta Bloomberg ta samu kwafen wasikar.

Amurka da kawayenta na kasashen Turai suna fuskantar takun saka da juna game da batun yarjejeniyar nukiliyar Iran. Kungiyar tarayyar Turai ta jaddada goyon bayanta ga yarjejeniyar nukiliyar duk da irin matsin lambar da take fuskanta daga Amurka kan batun nukiliyar Iran. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China