Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta kaddamar da samfurin jirgin kasa na gwaji mai matukar sauri dake tafiyar km 600 cikin sa'a 1
2019-05-24 13:22:36        cri

Kasar Sin ta kaddamar da samfurin jirgin kasa mai amfani da karfin maganadisu mai matukar saurin dake gudun km 600 cikin sa'a 1, jiya Alhamis a birnin Qingdao dake gabashin kasar.

Wannan samfurin jirgin na farko a kasar Sin gagarumin ci gaba ne ga kasar a fannin sufurin jiragen kasa masu matukar sauri.

Shugaban ayarin masu bincike kan kera jirgin kasa kuma mataimakin babban injiniya na kamfanin CRRC Qingdao Sifang da suka kera jirgin, Ding Sansan, ya ce samfurin jirgin na gwaji, wanda ke da tarago daya, zai iya dubawa da amfani da muhimman fasahohi da manyan tsarukan dake tattare da jirgin kasa mai amfani da karfin maganadisu, wanda zai samar da tushen fasahohin da da za a yi amfani da su a nan gaba.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China