![]() |
|
2019-05-07 06:51:27 cri |
A yau ne aka bude taron kolin fasahohin zamani na kasar Sin karo na biyu a Fuzhou, babban birnin lardin Fujian dake gabashin kasar, inda aka baje kolin sabbin na'urorin zamani da suka karade sassa da kamfanonin gwamnatin kasar.
Cikin fasahohin da ake amfani da su a bikin dake gudana a birnin Fuzhou, sun hada da motoci marasa matuka da na'urorin tsaro na tantance fuska zuwa fasahar sadarwa ta 5G. Za kuma a gabatar da rahoton bincike game da nasarar da kasar Sin ta samu a fannin kera fasahohin zamani a shekarar 2018.(Ibrahim)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China