Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Afrika ta kudu ya koka game da yadda rashin aikin yi ke addabar matasan kasar
2019-06-17 10:48:11        cri
Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya ce matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasan kasar ta kai matsayin koli kuma tana bukatar a dauki matakan gaggawa wajen shawo kanta.

"Sama da rabin matasan Afrika ta kudu tsakanin shekaru 15 zuwa 24 na haihuwa ba su da aikin yi," shugaban ya furta hakan ne a lokacin bikin Ranar Matasa.

Ramaphosa ya bukaci bangarorin masu zaman kansu da su kawo dauki, kuma su hada kai da bangaren gwamnati wajen warware matsalar rashin aikin yi a kasar.

"Idan muna son shawo kan wannan matsalar, ya kamata mu kara yin hadin gwiwa da hukumomi masu zaman kansu domin a samu damar bullo da guraben ayyukan yi ga matasa wadanda a shirye suke su koya, kuma su yi aiki tukuru domin kyautata makomar rayuwarsu a nan gaba," in ji shi.

Ramaphosa ya yi alkawarin samar da tsarin ilmi kyauta ga dalibai marasa galihu.

"Wannan ne dalilin da ya sa aka kara kudin tallafin dalibai a kasafin kudi na kasa daga rand miliyan 70 kwatankwacin dala miliyan 20 a shekarar 1994 zuwa rand biliya 1.5 kwatankwacin dala miliyan 110 a shekarar 2018," in ji shugaban.

Ana gudanar da Ranar Matasa ne a ranar 16 ga watan Yuni domin tunawa da al'amarin da ya faru ga dubban matasa da suka yi zanga zangar nuna adawa da gwamnatin wariyar launin fata a shekarar 1976. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China