Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Afrika ta kudu ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar
2019-05-16 13:38:56        cri
Duba da yadda kasar Afrika ta kudu ke fama da matsalar kodamar tattalin arziki, da rashin ayyukan yi, shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya fada a taron masu zuba jari na Goldman Sachs cewa, gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen yin garambawul ga sha'anin tattalin arzikin kasar domin kyautata yanayin tattalin arzikin kasar da samar da guraben ayyukan yi.

A lokacin tattaunwa da babban jami'in kamfanin Goldman Sachs na kudu da hamadar saharar Afrika, Colin Coleman, a Johannesburg, Ramaphosa ya ce, warware matsalar tattalin arzikin a karon farko zai magance manyan matsalolin dake damun kasar.

"Babbbar matsalar dake damun kasarmu shi ne ja da bayan tattalin arziki, kowane al'amari ya ta'allaka ne kan tattalin arziki. Muna bukatar mu mayar da hankali kan yadda za'a farfado da tattalin arziki, babban nauyin dake wuyanmu shi ne samar da guraben ayyukan yi," in ji shi.

Tun bayan da aka zabi Ramaphosa a matsayin shugaban kasar a jam'iyyar ANC, masana tattalin arziki sun yi ta nanata cewa wajibi kasar Afrika ta kudu ta fito fili ta bayyana matsayarta.

To sai dai shugaban kasar ya ce, tsare-tsaren da ya tanada suna da matukar alfanu wajen janyo hankalin masu zuba jari da kuma tunkarar manyan kalubalolin dake ciwa fannin zuba jari a kasar tuwo a kwarya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China