Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afrika ta kudu ta shirya karbar bakuncin shugabannin duniya mahalarta bikin ratsar da shugaban kasa
2019-05-24 11:17:28        cri
Ministan harkokin 'yan sanda na kasar Bheki Cele, ya bayyana a jiya Alhamis cewa, shirye shirye sun kammala don gudanar da bikin rantsar da shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa, an tsaurara matakan tsaro a birnin Pretoria saboda bikin na ranar Asabar.

Cele ya bayyanawa 'yan jaridu cewa, 'yan sanda sama da 2,500 ne za'a tura a yankunan dake ciki da wajen filin wasa na Loftus Versfeld da za'a gudana da bikin.

Ministan ya bayyana cewa sama da shugabannin kasashe 40 da wasu mutane 34,000 ne za su halarci bikin rantsar da shugaban kasar.

Ministan ya kara da cewa, "An kafa wani cikakken tsari domin tabbatar da ganin an gudanar da bikin cikin nasara. Jami'an 'yan sanda da sauran jami'an tsaron fararen hula za su gudanar da aiki tare domin tabbatar da ganin an aiwatar da bikin cikin nasara a filin wasan."

Cele ya ce, Ramaphosa zai yiwa al'ummar kasar jawabi bayan kammala rera taken kasar. Wannan zai biyo bayan faretin girmamawa ne wanda 'yan makarantar mata ta Pretoria Girls High School za su gudanar.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China