![]() |
|
2019-07-19 10:23:47 cri |
Da yake jawabi a fadar White House, Trump ya ce, jirgin ruwan yakin Amurkar samfurin USS Boxer, ya lalata jirgin yakin Iran maras matuki, bayan da ya yiwa jirgin ruwan yakin Amurkar barazana ta hanyar yin shawagi a nisan da bai gaza yadi 1,000 ba a samansa.
Trump ya ce, jirgin Iran maras matukin yana barazana ga lafiyar jirgin ruwan yakin na Amurka da matukansa, inda ya kira kakkabo jirgin a matsayin matakin kare kai.
Daga bisani, babban mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, Jonathan Hoffman ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, jirgin ruwan yakin Amurka, ya kakkabo jirgin Iran maras matuki ne da misalin karfe 10 na safe agogon wurin, lokacin da yake kokarin yada zango a mashigin Hormuz.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China