Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daukewar wutar lantaki a New York ta shafi mutane 72,000
2019-07-15 11:17:07        cri

Kamfanin samar da ababan more rayuwa na Con Edison, ya bayyana cewa, kimanin mutane 72,000 ne daukewar wutar lantarki da aka samu a birnin Manhattan dake New York ta shafa.

Kamfanin wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce, daukewar wutar ta faru ne da misalin karfe 6.47 na yammacin ranar Asabar, agogon wurin, lamarin da ya shafi na'urorin raba wutan lantarki da dama dake yankin, abin da ya kai ga dubban kwastomin kamfanin zama cikin duhu.

Yankunan da daukewar wutar ta shafa, ya kama daga titin na 40 dake kudu zuwa titin na 72 dake arewacin birnin da kuma yanki na biyar zuwa kogin Hudson.

Sai dai an yi nasarar dawo da wutan lantarkin a galibin yankunan da lamarin ya shafa kafin tsakar daren ranar Asabar.

Rahotanni na cewa, daukewar wutar ta faru ne a daidai wannan rana da birnin ya kasance cikin duhu sakamakon makamaiciyar daukewar wutar lantarkin a shekarar 1977. A halin da ake ciki, magajin garin birnin New York Bill de Blasio, ya kawar da zargin da wasu ke yi game da hannun 'yan ta'adda a lamarin. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China