![]() |
|
2019-07-09 14:27:05 cri |
Mike Pence ya bayyana haka ne da yake jawabi ga taron shekara-shekara na kungiyar mabiya addinin Kirista masu goyon bayan Isra'ila, da aka yi jiya a birnin Washington.
Jawabin nasa na zuwa ne sa'o'i bayan Tehran ta sanar da kara yawan sinadarinta na Uranium zuwa kaso 4.5, wanda ya zarce kaso 3.67 na iyakar da yarjejeniyar nukiliyar kasar ta gindaya.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo da mai bada shawara kan tsaron kasar John Bolton, dukkansu masu sukar Iran, su ma sun jaddada wannan matsaya ta mataimkain shugban kasar a jawabin da suka yi yayin taron.
Shekara guda bayan janyewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar, ita ma Iran ta janye a ranar 8 ga watan Mayu tare da barazanar daukar karin matakai ko da an gagara kare muradunta karkashin yarjejeniyar. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China