Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoton bincike: Kasar Amurka ta fi samar da shara a duniya
2019-07-06 15:53:41        cri
Rahoton da aka gabatar game da wani binciken da aka yi kan yanayin samar da shara a kasashe daban daban ya nuna cewa, kasar Amurka ta fi samar da shara a duniya, inda yawan sharar da ta samar ya ninka wani matsakaicin matsayi na duniya har sau 3.

An gudanar da binciken ne bisa nau'ikan shara da ake samarwa, wato nau'ikan shara irin na yau da kullum, da na leda, da ragowar abinci, gami da shara mai guba. Sa'an nan an gano cewa jama'a da kamfanonin Amurka sun samar da mafi yawan shara a dukkan wadannan nau'ika 4.

Bisa samar da shara mai nauyin kilo 773 kan ko wane mutum a shekara guda, kasar Amurka ta samar da kashi 12% na sharar duniya, yayin da yawan al'ummar kasar ya kai kashi 4% kadai na daukacin al'ummar duniya.

A nasu bangaren, kasashen Sin da Indiya dake da al'ummar da ta kai fiye da kashi 36% na daukacin al'ummar duniya, na samar da sharar da ta kai kashi 27% na sharar da ake samu a duk duniya.(Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China