Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mai yiwuwa jiragen Boeing 737 MAX ba za su koma aiki ba sai zuwa shekarar 2020
2019-07-15 13:52:40        cri

Gwamnatin kasar Amurka da kamfanin Boeing sun ce akwai yiwuwar jiragen sama masu samfurin Boeing 737 MAX ba za su koma jigilar fasinjoji ba sai zuwa shekarar 2020, domin za a dauki lokaci wajen gyaran manhajar tukin jirgin da kammala sauran wasu ayyuka.

A cewar jami'an hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Amurka da shugabannin kamfanin Boeing, ana sa ran jiragen su koma aiki a watan Janairun 2020, watanni 12 cif bayan kamfanin ya gabatar da kudurinsa na farko na maye gurbin manhaja mai sarkakkiya da aka yi munanan haddura da ita.

An dakatar da tashin jiragen a fadin duniya tun a watan Maris na bana, bayan samfurin jirgin 2 sun hatsari a lokuta mabambanta, da suka hada da na Indonesia a watan Oktoban bara da na Habasha a watan Maris na bana, inda suka yi sanadin asarar rayuka 346. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China