Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin kasar Sin a MDD ya yi kira da a taimakawa kasashen da suka yi fama da tashin hankali
2019-07-19 09:37:21        cri
Mataimakin wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya yi kira ga kasashen duniya da su mayar da hankali wajen samar da kwarewa a kasashen da suka yi fama da tashe-tashen hankula ta yadda za su gina kansu da kansu.

Wu ya bayyana hakan ne yayin taron kwamitin sulhun MDD game da karfafa alaka ta yadda irin wadannan kasashe za su samu nasarar farfado da kansu.

Ya ce, kasashe da dama sun fara aiwatar da matakan raya kansu, da na tabbatar da zaman lafiya da bunkasuwa na dogon lokaci, bayan kawo karshen tashin hankalin da suka fuskanta.

Jami'in na kasar Sin ya ce, ya kamata MDD da kasa da kasa su baiwa irin wadannan kasashe taimako da goyon bayan da ya dace.

Wu Haitao ya kuma jaddada muhimmancin yin hadin gwiwa, yana mai cewa ya kamata MDD da ilahirin al'ummomin kasa da kasa, dake taimakawa kasashe wajen farfadowa bayan tashin hankali, su karfafa sadarwa da hada kai da kungiyoyin yankuna da na shiyya, su kuma sakarwa kungiyoyin tarayyar Afirka, da kasashen Larabawa da ASEAN da sauransu, ta yadda za su taka rawar da ta dace a harkokin shiyya-shiyya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China