Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi hasashen ya zuwa 2050, 2 bisa 3n al'ummar duniya za su yi rayuwa a birane
2019-07-17 11:02:36        cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce kaura zuwa birane shi ne babban abun da ake ya yi, inda aka yi hasashen ya zuwa 2050, kusan 2 bisa 3n al'ummar duniya za su koma rayuwa a yankunan birane.

A jawabinsa yayin wani taro da aka yi domin cika shekaru 25 da gudanar da taron kasa da kasa kan al'umma da ci gaba, Antonio Guterres ya ce muradun ci gaba masu dorewa da sauyin yanayi, za su kara dogaro kan yadda aka yi nasarar kula da karuwar al'umma a birane.

Ya ce karuwar al'umma alama ce ta ci gaban bil adama, tunda ta na nufin tsawon rayuwar mutane na karuwa kuma suna cikin koshin lafiya, sannan yana bada gudunmuwa wajen kara samar da kayayyaki da amfani da su a duniya.

Ya ce wannan dalili ne na daidaita ayyukan samar da kayayyaki da halayyar amfani da su domin kaucewa abun da zai iya biyo baya ga rayuka da zaman rayuwa, musammam ta masu rauni. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China