Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararrun Sin: tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba yadda ya kamata a watanni 6 na farkon bana
2019-07-16 15:57:56        cri

Wasu kwararrun kasar Sin sun bayyana a jiya Litinin a nan birnin Beijing cewa, a cikin watanni shida na farkon shekarar da muke ciki, yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasa wato GDP a takaice, ya karu da kashi 6.3 cikin 100 bisa na makamancin lokacin raba, wanda ya dace da hasashen da aka yi. An kuma tabbatar da zaman karko game da yanayin samun guraban ayyukan yi, kana tsarin tattalin arzikin kasar ya ci gaba da kyautatuwa, hakan ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar ta Sin na samun ci gaba yadda ya kamata.

A jiya Lititin 15 ga wata ne, aka nuna yanayin da tattalin arikin kasar Sin yake ciki a watanni shida na farkon shekarar 2019. Alkaluman da hukumar kididdigar kasar ta fitar, sun nuna cewa, yawan GDPn da kasar ta samu a cikin watannin shida ya wuce RMB triliyan 45, karuwa kashi 6.3 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.

A yayin taron dandalin tattaunawa game da nazarin yanayin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki a tsakiyar shekarar da aka shirya a wannan rana, mamban kwamitin fasahohi na cibiyar yin cudanyar harkokin tattalin arziki ta kasa da kasa ta kasar Sin, kuma babban masani a fannin tattalin arziki na bankin ZYB, mista Wang Jun ya bayyana cewa, a cikin watanni shida na farkon shekarar da muke ciki, sabbin mutanen da suka samu aikin yi sun karu zuwa miliyan 7.37, wato an cimma burin da aka tsaida na kashi 67 cikin 100 na shekarar da muke ciki, wannan mataki ya samu gagarumin yabo kan ci gaban tattalin arzikin kasar a cikin wadannan watanni shida. Wang Jun ya kara da cewa,

"Ba abu ne mai sauki ba a cimma burin kashi 67 cikin 100 na shirin da aka tsara a cikin watanni shida na farkon shekarar da muke ciki, ko da yake yawan mutanen da suka rasa ayyukan yi ya karu kadan a cikin watan Yuni, amma duk da haka, tattalin arzikin kasar Sin yana gudana yadda ya kamata. Duk da cewa, an samu tabbaci a bangaren samar da aikin yi, babu wata matsala ba ce idan karuwar tattalin arziki ta dan fuskanci tangal-tangal. Don haka, ana iya cewa, wannan wata alamar yakini ce ta farko."

Kwararru mahalarta taron dandalin tattaunawar sun kuma yi nazarin cewa, sana'ar hidima ta karu da kashi 7.0 cikin 100 a cikin watanni shida na farkon bana. Ban da wannan kuma, ingantuwar fannin sana'ar kere-kere ta zamani ta sa fannin ya samu karuwar kashi 9 cikin 100, wadda karuwarta ya fi na dukkan masana'antu sauri da kashi 3 cikin 100. Kana yawan jarin da aka zuba a fannonin al'umma, masana'antun zamani, yin gyare-gyare kan sana'ar kere-kere ya karu da sama da kashi 10 cikin 100. Dukkan alkaluman sun nuna cewa, a yanzu haka, tsarin tattalin arziki a kasar Sin na ci gaba da kyautatuwa. Game da haka, shugabar cibiyar binciken kasuwar hada-hadar kudi ta kasar Sin madam Tan Yaling ta bayyana cewa,

"Tattalin arzikin kasar yana tafiya yadda ya kamata a cikin watanni shida na farkon bana, kuma wannan ba abun mamaki ba ne, an cimma nasarar kyautata tsarin tattalin arzikin kasar, ciki har da yadda aka samu ingatuwar sabbin masana'antu, da yadda abubuwan hawa masu amfani da sabbin makamashi suka karu a tsakanin kashi 7.7 da kashi 34 cikin 100 bi da bi, ana iya cewa, an aiwatar da manufofin da gwamnatin kasar ta tsara a fannin neman ci gaban tattalin arzikin kasar sakamakon ci gaban sabbin masana'antu yadda ya kamata."

An yi tsokacin cewa, tun daga shekarar da ta gabata, an samu raguwar karuwar tattalin arzikin duniya, da ma cinikayyar kasa da kasa, bisa wannan yanayin da ake ciki, ko da yake saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya ragu kadan, amma duk da haka, tattalin arzikin kasar na gudana yadda ya kamata. Mamban kwamitin fasahohi na cibiyar yin cudanyar harkokin tattalin arziki ta kasa da kasa ta kasar Sin, kuma babban masani a fannin tattalin arziki na bankin ZYB, mista Wang Jun ya bayyana cewa, bayanan dake nuna yadda tattalin arziki ke tafiya, ana iya fahimtar alamar farfadowar tattalin arzikin. Wang Jun ya kara da cewa,

"Ma'aunin harkokin kudi, da saurin karuwar tattara kudi a fannin zamantakewar al'umma ya wuce hasashen da aka yi, inda ya kai kashi 10.9 cikin 100, hakan ya nuna cewa, akwai yiwuwar nan gaba tattalin arzikin ya farfado yadda ya kamata. Ban da wannan kuma, yawan kudin musanya da aka tanada ya soma karuwa a watan Yuni. Wata alama mai yakini ta daban ita ce, yawan motocin daukar fasinja da aka sayar a watan Yuni ya karu da kashi 4.9 cikin 100, wannan ne karo na farko da aka samu karuwa a wannan fannin a cikin watanni 13 da suka gabata. A gani na, duk wadannan abubuwan da na zayyana, za su ci gaba da taka rawa kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a cikin watanni shida masu zuwa." (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China