Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ribar da kayayyakin kananan kamfanoni sama da 100 na kasar Sin suka samar ya kasance a kan gaba a duniya
2019-07-15 10:34:56        cri

Wani rahoto da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar, ya nuna cewa, ribar da kasar ta samu daga kayayyakin da kananan kamfanonin kasar sama da 100 ke kerawa, wadanda suka hada da kekune da batura da kujeru da tebura da gadaje, ta kasance na farko a duniya.

Rahotanni na nuna cewa, a cikin sama da shekaru 70 da suka gabata, kayayyakin da kamfanonin kasar Sin suke kerawa sun bunkasa cikin sauri, inda karfin masana'antun ya ninka sau 970.6 daga Yuan biliyan 12, kwatankwancin dala biliyan 1.75 a shekarar 1952 zuwa Yuan Tiriliyan 30.52 a shekartar 2018, karuwar kimanin kaso 11 cikin 100 bisa makamancin shekarar da ta gaba ce ta.

Bugu da kari rahoton ta bayyana cewa, tasirin bangaren masana'antun kasar Sin a duniya, shi ma ya haifar da canjin da ba a taba ganin irinsa ba a tairihi. A shekarar 2010, bangaren masana'antun kera kayayyaki na kasar Sin ya dara na Amurka, inda a karon farko ya kasance bangaren masana'antu mafi girma a duniya , kana ya ci gaba da rike wannan matsayi tun wancan lokaci.

A daya hannun kuma,a shekarar 2017 ribar da hannayen jarin bangaren masana'antun kera kayayyakin kasar ya samu ya kai kaso 27 cikin 100, matakin da ke nuna cewa, ya kasance muhimmin tubalin dake bunkasa ci gaban masana'antun duniya baki daya. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China