Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tattalin arzikin Sin na fadada cikin daidaito duk da kalubale da ya fuskanta
2019-07-15 19:46:30        cri

Ma'aunin tattalin arzikin kasar Sin na GDP ya karu, da kaso 6.3 bisa dari, a rabin farko na shekarar nan ta 2019, inda adadin yawan sa ya kai yuan tiriliyan 45.09, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 6.6. Hakan dai na kunshe ne cikin wasu alkaluma da hukumar kididdiga ta kasar NBS ta fitar a Litinin din nan.

Da yake tsokaci game da alkaluman yayin wani taron manema labarai da ya gudana a yau, kakakin hukumar ta NBS Mr. Mao Shengyong, ya ce tattalin arzikin kasar Sin na kara daidaita sannu a hankali, yana kuma kan mizani mai inganci, ya kuma samu ci gaba a wasu sassa.

Ya ce karuwar kaso 6.3 bisa dari da aka samu a ma'aunin na GDP, ya zo a daidai gabar da ake fama da tafiyar hawainiya a yanayin tattalin arzikin duniya, da raunin fadadar cinikayyar kasa da kasa, da matsi a kasuwannin cikin gida, wanda hakan ya sanya har yanzu, Sin ta kasance kasa da tattalin arzikin ta ya dara na sauran kasashen duniya fadada.

Mao ya ce alkaluman na watanni 6n farkon shekarar nan, sun nuna irin karfi da ginshikin tattalin arzikin kasar Sin ke da shi, wanda ya kai ga cimma hasashen ta na ci gaba a shekarar.

Kaza lika jami'in ya bayyana cewa, duk da yake tattalin arzikin kasar ya ci karo da matsi daga wasu sassa na waje, a watanni 6 da ake ciki na karshen shekarar, jigon kasar na samun bunkasar tattalin arziki bai sauya ba, kuma gwamnatin Sin na da zarafi mai fadi, na kara inganta tsare tsaren raya tattalin arzikin ta.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China