
Alkaluman kididdigar da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar a yau Litinin, sun nuna cewa, a cikin watanni shida na farkon shekarar da muke ciki, yawan kudin da aka samu daga sarrafa dukiyar kasa wato GDP ya karu da kashi 6.3 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara, inda a rubu'i na farko na wannan shekara, an samu karuwar kashi 6.4 cikkin dari, kana a rubu'i na biyu an samu karuwar kashi 6.2 cikin dari. Wannan na nuna cewa, tattalin arzikin kasar ta Sin yana tafiya yadda ya kamata. (Bilkisu)