Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararrun kungiyar OECD suna sa rai ga makomar tattalin arzikin Sin
2019-05-27 14:55:55        cri

Kwanakin baya, kungiyar hadin kai don raya tattalin arzikin duniya ta OECD ta bayar da rahoton hasashen tattalin arzikin duniya na shekarar 2019, inda ake ganin cewa, sakamakon yin kwaskwarima kan tsarin tattalin arzikin da kasar Sin ke yi, a 'yan shekaru masu zuwa, akwai yiyuwar saurin karuwar tattalin arzikin kasar ya samu raguwa kadan, amma zai ci gaba da karuwa a nan gaba.

Kungiyar hadin kai don raya tattalin arzikin duniya ta OECD wadda ke da mazauni a Paris, babban birnin kasar Faransa ta fitar da rahoton hasashen tattalin arzikin duniya na shekarar 2019 a kwanakin baya, inda aka yi hasashe kan karuwar tattalin arzikin duniya da ma wasu muhimman kasashe da yankuna masu saurin ci gaban tattalin arziki a bana da ma shekara mai zuwa. Game da tattalin arzikin kasar Sin, ofishin nazarin manufofin tattalin arzikin kasar Sin na kungiyar OECD ya yi hasashe cikin rahoton, cewar saurin karuwar GDP da kasar Sin za ta samu zai kai kashi 6.2 cikin dari a shekarar 2019, yayin da jimillar za ta kai kashi 6 cikin dari a shekarar 2020.

Ko da yake kasar Sin na fuskantar rashin tabbas kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da tsanantar yanayin cinikayyar kasa da kasa, da ma aikin yin kwaskwarima ga tsarin tattalin arzikinta, rahoton ya nuna cewa, yawan matsakaicin kudin shiga da Sinawa ke samu yana karuwa ba tare da tangarda ba, kana ana samun karuwar bukatun cikin gida yadda ya kamata, lamarin da ya zama muhimmin dalilin ga bunkasar tattalin arzikin Sin lami lafiya. Ban da wannan kuma, bisa kididdigar tattalin arzikin da gwamnatin kasar Sin ta bayar a kwanakin baya, an ce, a watanni uku na farkon shekarar nan da muke ciki, yawan gudummawar da kudin kashewa ya bayar ga karuwar tattalin arziki ya kai kaso 65.1, lamarin da kara aza harsashi mai inganci sosai. Game da wannan batun, Dr. Margit Molnar, shugabar ofishin nazarin manufofin tattalin arzikin Sin na kungiyar OECD ta bayyana cewa, yadda kasar Sin ke yi na kara kason kudin kashewa a cikin gudummawar da ake bayar ga karuwar tattalin arziki ya yi daidai. Tana mai cewa,

"Wannan matakin da kasar Sin ta dauka ya yi daidai. Dole ne a kara kason kudin kashewa yayin da kasar Sin ke kokarin bunkasa har ta zama kasa mai sukuni. Don haka ya zama dole a kara kason kashe kudi a cikin gudummawar bunkasar tattalin arziki. Ina zaton cewa, lallai kasuwar kashe kudi ta Sin na da sirri mai karfin matuka."

Ana ci gaba da rigingimun cinikayya tsakanin Sin da Amurka yanzu, ana damuwa kan yadda jarin waje zai janye jiki daga kasar Sin. Amma bisa alkaluman da ma'aikatar kasuwancin Sin ta bayar, an ce, a watanni hudu na farkon shekarar bana, yawan kudaden ketare da kasar Sin ta yi amfani da su ya zarce Yuan biliyan 305, wanda ya karu da kaso 6.4 bisa na bara. Dangane da batun, Dr. Margit ta furta cewa, akwai wasu dalilan da suka sa jarin waje ke sa rai ga makomar tattalin arzikin Sin.

"Yawan karuwar tattalin arzikin Sin ya fi na sauran kasashe, ba ma a bana kadai ba, zai tafi a haka a cikin gajere da matsakaicin lokaci masu zuwa. Lamarin da ya sa za a ci gaba da zubawa Sin jari, musamman ma bayan kyautata muhallin kasuwanci ga baki da kasar Sin ta yi."

A halin yanzu ma dai, kasar Sin na ci gaba da aiwatar da bude kofa ga waje. Dr. Margit ta ce, matakan da kasar Sin ta dauka na kara bude kofarta a fannin harkokin kudi, da ma inganta hadin gwiwa tare da ketare wajen kiyaye ikon mallakar ilmi, da ma kara shigo da kayayyaki da ayyukan ba da hidima kasuwarta, dukkansu za su taimakawa tattalin arzikin Sin wajen samun dauwamammen ci gaba cikin dogon lokaci. Game da bunkasar tattalin arzikin Sin a nan gaba, Dr. Margit ta ce, tana sa rai ga batun. Ta kara da cewa,

"Ina ganin cewa, kasar Sin na da kyakkyawar makoma wajen samun bunkasar tattalin arzikin a cikin shekaru 10 zuwa 20 masu zuwa. Amma abin da nake so in jaddada shi ne, aikin yin kwaskwarima ga tsarin tattalin arziki na da matukar muhimmanci."(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China