Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang: Tattalin arzikin Sin na da inganci ya kuma daidaita a farkon shekarar bana
2019-07-02 15:18:19        cri
A Talatar nan ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya sanar da cewa, tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da kasancewa cikin daidaito, da inganci a watanni shida na farkon shekarar bana. Mr. Li ya bayyana hakan ne, cikin jawabin da ya gabatar, a wajen bude taron tattalin arziki na shekara-shekara na Davos, a birnin Dalian na kasarsa.

Firaminista Li ya ce alkaluman tattalin arziki na nuna cewa, tsakanin wadannan watanni, an cimma burin raya tattalin arzikin Sin bisa hasashen da aka yi tun da fari.

Ya ce a watan Mayu, alkaluman rashin aikin yi sun yi kasa da kusan kaso 5 bisa dari, kana a duk rana, an rika yiwa kamfanoni 18,900 rajista cikin watanni biyar na farkon shekarar.

A wani ci gaban kuma, Li ya ce tattalin arzikin Sin ya fuskanci matsi, da yanayin rashin tabbas daga ketare, amma duk da haka, kasar ta shiryawa irin wadannan yanayi da ka iya tasowa ta kuma tunkari dukkanin kalubalen.

Ya kara da cewa, Sin na da babbar kasuwa, da tarin albarkatun jama'a, da dubban rukunonin masana'antu masu saurin bunkasuwa, don haka tattalin arzikinta na iya jure duk wani matsi, yana kuma da damar sauya salo bisa bukatar da ake da ita. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China