![]() |
|
2019-07-12 15:37:49 cri |
Hukumar kwastan ta kasar Sin ta fitar da wata kididdiga a yau Jumma'a dake cewa, a farkon rabin shekarar bana, yawan kudin dake shafar cinikayyar shige da fice ya kai kudin Sin RMB triliyan 14.67, wanda ya karu da kashi 3.9 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara. Daga cikinsu kuma, yawan kudin dake shafar cinikin fitar da kayayyaki ya kai RMB biliyan 7950, wanda ya karu da kashi 6.1 cikin dari, yayin da a fannin cinikin shigo da kayayyaki kuma, wannan adadi ya kai RMB biliyan 6720, wanda ya karu da kashi 1.4 cikin dari. Rarar kudin da aka samu kuma ta kai RMB biliyan 1230, wanda ya habaka da kashi 41.6 cikin dari. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China