Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manzon kasar Sin ya yi kira ga kasashen duniya da su kara taimakwa Somaliya
2019-05-23 10:20:24        cri

Karamin jakada kana jami'in tsare-tsaren siyasa na tawagar kasar Sin dake MDD Yao Shaojun, ya yi kira ga kasashen duniya, da su kara taimakawa kasar Somaliya a fannin tsaro da jin kai da inganta rayuwar jama'a da tattalin arziki.

Da yake yiwa zaman kwamitin sulhun MDD karin haske, jami'in na kasar Sin ya bayyana cewa, Somaliya, kasa ce mai muhimmanci a yankin kahon Afrika. Tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar a hankali a kasar, ya dace da muradun al'ummar shiyyar da ma kasashen duniya baki daya.

Ya ce, a halin da ake ciki yanzu, yanayin da ake ciki a kasar na da sarkakiya, sannan kasar tana fuskantar kalubale a sassa da dama. Don haka, ya kamata kwamitin sulhu da ita kanta MDD da daukacin al'ummar kasa da kasa, su ba ta goyon baya da taimakon da ya dace.

Ya kuma bukaci a mutunta 'yancin gwamnatin tarayyar kasar na tafiyar da harkokin cikin gidanta, da inganta tattaunawa da tsare-tsare da gwamnatin Somaliya,da martaba shirin da ta bullo da shi, da inganta karfinta na samun ci gaba da kanta.

Jami'in na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan shirin kasar Somaliya na samar da zaman lafiya tare da taka muhimmiyar rawa wajen ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma ci gaba ya tabbata a kasar ta Somaliya da ma yankin kahon Afirka baki daya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China