![]() |
|
2019-06-14 19:54:22 cri |
Hukumar kididdigar ta kasar Sin, ta fitar da bayanin halin bunkasuwar tattalin arzikin Sin a watan Mayu, inda wasu alkaluma suka shaida cewa, tattalin arzikin Sin na samun bunkasuwa yadda ya kamata a wannan wata.
Kakakin hukumar Fu Linhui ya bayyana a gun taron manema labarai da aka yi a yau Juma'a, a ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, na cewa, a watan na Mayu, yawan kudin da aka samu wajen sayar da kayayyakin yau da kullum ya kai RMB Yuan biliyan 3295.6, adadin da ya karu da kashi 8.6 bisa dari idan an kwatanta da makamancin lokaci na bara. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China