Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin a MDD ya bukaci kasa da kasa su mutunta 'yancin kasar Burundi game da zabenta
2019-06-15 15:36:21        cri

A ranar Juma'a wakilin kasar Sin a MDD ya bukaci kasashen duniya da su nuna cikakken mutuntawa ga ikon da kasar Burundi ke da shi game da lamarin shugabancin kasar da 'yancin gudanar da zaben kasar kuma su ba ta dukkan tallafin da gwamnatin ke bukata.

Ya kamata kasashen duniya su bada fifiko wajen kokarin samar da yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali ga kasar, in ji mista Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, wanda ya bayyana hakan yayin taron kwamitin sulhun MDD.

"Zabuka batu ne da ya shafi al'amurran cikin gidan kasar," in ji wakilin na Sin.

A cewar jakada Wu, a karshen shekarar bara ne, gwamnatin kasar Burundi ta fara shirye-shiryen gudanar da zabukanta na shekarar 2020 ta hanyar tuntubar dukkannin jam'iyyun siyasar kasar. Tuni ta riga ta shirya wasu hanyoyi da tsare-tsaren da za su taimaka mata wajen tattara dukkan kudaden da ake bukata wajen shirya zaben kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China