Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ya yi maraba da tattaunawar da shugabannin Amurka da Koriya ta Arewa suka yi a Panmunjom
2019-07-01 19:37:52        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana yau Litinin 1 ga watan Yuli a nan Beijing cewa, shugabannin kasashen Amurka da Koriya ta Arewa sun yi tattaunawar sada zumunta, inda aka samu sakamako mai kyau, tattaunawar da aka yi maraba da ita sosai. Kasar Sin na fatan sassa daban daban masu ruwa da tsaki, za su yi amfani da kyakkyawar dama wajen lalubo bakin zaren daidaita batutuwan da suka sa kulawa a kai, a kokarin kara azama kan samun sabon ci gaba a fannin kawar da nukiliya a zirin Koriya a siyasance.

Jiya Lahadi ne shugabannin kasashen Koriya ta Arewa, da Amurka da Koriya ta Kudu, suka gana da juna karo na farko a yankin da aka hana girke dakaru a tsakanin kasashen Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China