Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta samar da gudummawar hatsi ga kasar Kenya don tinkarar bala'in fari
2019-06-11 11:10:29        cri

 

Jakadan Sin dake kasar Kenya Wu Peng ya bayyana a jiya cewa, gwamnatin kasar Sin ta samar da gudummawar hatsi da darajarsu ta kai Yuan miliyan 80 ga kasar Kenya don taimaka mata wajen tinkarar bala'in fari da ya fi tsanani a cikin shekaru 38 da suka gabata. Kashin faro na kayayyaki sun isa birnin Mombasa a ranar 19 ga watan Mayu, wadanda aka raba su ga mutane masu fama da bala'in, kuma za a fara yin jigilar kayayyaki kashi na biyu da nauyinsu ya kai ton 1500 tun daga karshen wannan wata.

Jakada Wu Peng ya bayyana cewa, bayan da kasar Kenya ta samu 'yancin kai, Sin ta taimaka mata da ayyuka kimanin 100 ta hanyoyin gudummawar kyauta, da rancen kudi ba tare da ruwa ba, da rancen kudi mai rangwame da sauransu, hakan ya sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma da zaman rayuwar jama'ar kasar. A matsayin daya daga cikin manyan abokan kasar Kenya, Sin za ta maida hankali ga manyan ajenda hudu na kasar musamman sha'anin kera kayayyaki yayin da take samar da gudummawa ga kasar Kenya. Kana kasashen biyu sun fara horar da malamai dake da kwarewar sana'a don inganta karfin bada ilmin sana'o'i da samar da ayyukan yi da kara kudin shiga a yankin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China