in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ECA ta bukaci kasashen Afirka da su bullo da matakan cin gajiyar yarjejeniyar AfCFTA
2019-05-05 15:32:13 cri
Hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afirka(ECA) ta yi kira ga kasashen Afirka da ma hukumomin nahiyar, da su tsara matakan da suka dace, yayin da yarjejeniyar cinikayya maras shinge ta Afirka ke dab da fara aiki.

Babban mai ba da shawara na hukumar dake aiki a cibiyar tsara manufofin cinikayya ta Afirka(ATPC) Adeyinka Adeyemi, ya yi kira ga kasashen Afirka da abokan hulda, da su shirya dandalin cinikayya da zuba jari wajen ganin yarjejeniyar da za ta fara nan da wasu makonni, ta kai ga nasarar da ake fata.

A ranar Larabar da ta gabata ce, kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta sanya wa'adin wata guda na ganin yarjejeniyar ta fara aiki a ranar 30 ga waTan Mayun wannan shekara, yayin da a farkon wannan mako kasashen Saliyo da Jamhuriyar Saharawi, su ka gabatarwa hukumar zartarwar kungiyar AU takardunsu na amincewa da yarjejeniyar.

A baya dai hukumar ECA, ta shirya wani dandalin cinikayya da zuba jari na shiyya game da yarjejeniyar ta AfCFTA, a birnin Legas dake tarayyar Najeriya, wanda ya hallara wakilai daga kasashen yammacin Afirka.

Hukumar ta kuma bayyana cewa, a yayin taron, masu ruwa da tsaki sun bayyana bukatar dake akwai ta shigo da sassa masu zaman kansu, a matsayin hanya mafi dacewa ta gano damammakin dake kunshe wannan yarjejeniya.

Manufar yarjejeniyar wadda kasashen Afirka 44 suka sanyawa hannu, lokacin da aka kafa ta a Kigali, babban birnin kasar Rwanda a watan Maris na shekarar 2018, ita ce, zirga-zirga tsakanin kasashen nahiyar ba tare da biyan haraji ba, matakin da zai taimaka wajen gina kananan sana'o'i da bunkasa harkokin cinikyaya tsakanin kasashen Afirka, da raya masana'antu gami da samar da guraben ayyukan yi.

Yarjejeniyar wadda kasashe da dama ke dauka a matsayin yarjejeniyar cinikayyar shiyya maras shinge a duniya, ta shafi sama da mutane biliyan 1.2 da GDPn da ya kai dala triliyan 2.5

A cewar hukumar ECA, an yi hasashen cewa, da zarar yarjejeniyar ta fara aiki, cinikayya tsakanin kasashen nahiyar za ta bunkasa da sama da kaso 52 cikin 100 nan da shekarar 2020.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China