Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
(Sabunta)Kasar Sin ta mallaki mafi yawan kayayyakin tarihi a duniya
2019-07-07 17:13:26        cri
Baraguzan gine-gine na tsohon garin Liangzhu na kasar Sin sun samu izinin zama cikin jerin sunayen kayayyakin tarihi da aka gada daga kaka da kakanni na duniya, a jiya Asabar, a wajen taron kayayyakin tarihi na duniya da ake yi a birnin Baku na kasar Azerbaijan. Wannan yasa yawan kayayyakin tarihi da aka gada daga kaka da kakanni na duniya da kasar Sin ta mallaka ya kai 55, wanda shi ne adadi mafi yawa a duniya.

A gun taron da aka shirya a wannan rana, an tattauna da kuma dudduba wasu baraguzan gine-ginen tarihi da dama na kasashen Sin, Iraki, Burkina Faso da dai sauransu. A yayin da ake duba baraguzan gine-ginen tarihin na Liangzhu, wakilai na kasashen Azerbaijan, Uganda, Norway da Zimbabwe da dai sauransu sun bada jawabi daya bayan daya, inda wakilin kasar Azerbaijan mai masaukin baki a taron ya bayyana cewa, baraguzai na Liangzhu sun nuna babban matsayin wayewar kai da kasar Sin da yankin gabashin Asiya suka dauka a shekaru 5000 da suka gabata.

Bayan kasar Sin ta cimma nasarar zama cikin jerin sunayen kasashe masu kayayyakin tarihi da aka gada daga kaka da kakanni na duniya, a madadin gwamnatin kasar Sin shugaban hukumar kula da harkokin kayayyakin tarihi na kasar Sin Liu Yuzhu ya nuna godiya sosai kan kasar Azerbaijan, ya kuma nuna cewa, kasar Sin za ta karfafa hadin kai da kasashen duniya, da nufin kara kiyaye kayayyakin tarihin na duniya.(Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China