![]() |
|
2019-07-06 17:19:29 cri |
Baraguzan gine-gine na tsohon garin Liangzhu na kasar Sin sun samu izinin zama cikin jerin sunayen kayayyakin tarihi da aka gada daga kaka da kakanni na duniya, a yau Asabar, a wajen taron kayayyakin tarihi na duniya da ake yi a birnin Baku na kasar Azerbaijan. Wannan ya sa yawan kayayyakin tarihi da aka gada daga kaka da kakanni na duniya da kasar Sin ta mallaka ya kai 55, wanda shi ne adadi mafi yawa a duniya. (Bello Wang)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China