Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Asusun tallafawa masu fama da talauci na Sin ya taimaka sosai ga aikin rage talauci a Afirka
2019-06-27 13:44:02        cri

Darektan sashin bunkasa harkokin kasa da kasa na asusun tallafawa masu fama da talauci na kasar Sin Wu Peng ya bayyana jiya Laraba a lardin Zhejiang dake gabashin kasar cewa, asusun ya samu dimbin nasarori wajen gudanar da ayyukan hadin-gwiwa na kawar da fatara a Afirka.

Wu ya ce, tun shekara ta 2007, asusun ya fara gudanar da ayyukan tallafawa mutanen da suke da bukata a kasashen Guinea Bissau da Sudan da Habasha da Uganda da Nambiya da Ghana, tare kuma da bada taimako wajen yaki da bala'in fari a yankin kahon Afirka gami da tinkarar cutar Ebola a yammacin nahiyar.

Har wa yau, asusun ya nuna himma da kwazo wajen taimakawa kasashen Afirka rage talauci ta hanyar inganta harkokin bada ilimi, musamman a kasashen Habasha da Sudan.

Bisa alkaluman da aka fitar, kawo yanzu, asusun tallafawa masu fama da talauci na kasar Sin ya zuba tallafin kudi sama da Yuan miliyan 162 a kasashen dake tasowa sama da 20 don taimakawa mutanen da suke da bukata.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China